ABNA24 : An soma azumin a kasashen da suka hada da Saudiyya, Turkiyya, Masar, Tunisia, Labanon, Hadaddiyar Daular Larabwa, Qatar, Bahreïn, da Yemen a gabas ta Tsakiyya.
A nahiyar Afrika kasashen da suka hada da Najeriya, Nijar, Sudan duk sun sanar da fara azumin bayan hango jinjirin watan da yammacin jiya Litini.
A Kasashen Iran da Oman, sai gobe za’a tashi da Azumin, saboda kasa hango jinjirin watan na Ramadan.
Azumin watan Ramadan na daya daga cikin shika-shikan Musulunci. Ana kwashe kwanaki ashirin da tara ko talatin ana yin azumin.
Kuma Musulmi kan kaurace wa ci da sha da kuma saduwa da iyali daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.
Ramadan wata ne mai alfarma da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu'o'i tare da neman gafara ga Mahalicci.
Wannan dai it ace shakara ta biyu da musulmi zasu azumci watan na Ramadan a cikin yanayi na fama da annobar korona, wanda ya sanya aka takaita ayyukan ibada musamman taruwa a masalatai domin gujewa yaduwar annobar.
342/